in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Syria sun kaddamar da hare hare a yankin Idlib
2018-09-10 10:50:28 cri
Rahotanni na cewa dakarun sojin Syria sun kaddamar da hare hare da dama a ranar Lahadi, a yankin da 'yan tawayen kasar suka yi tunga dake Idlib, da kuma wajen lardin Hama dake tsakiyar kasar.

Kungiyar dake sanya ido kan al'amura masu nasaba da kare hakkokin bil'adama ta Syria, ta ce an ga jiragen yaki na Rasha, da na Syria na barin wuta a yankunan lardin Hama, yayin da su kuma mayakan 'yan tawaye na "National Front for Liberation" masu sansani a yankunan Turkiya, ke kaiwa sojojin kasar ta Syria hare hare a lardin. Kungiyar mai samun mafaka a birnin London ta ce yawan hare hare ta sama da aka kaddamar kan yankin Idlib cikin kwanaki 3 ya kai 1,060.

A daya bangaren kuma, kamfanin dillancin labarai na Syria SANA, ya bayyana cewa, sojojin kasar Syria sun matsa kaimi wajen kaddamar da hare hare, kan yankunan da mayakan Nusra Front masu alaka da Al-Qida ke iko da su a lardin Hama.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China