Assad yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da ministan tsaron Iran Amir Hatami, wanda ke ziyarar aiki a kasar Syria, kana ya gana da manyan jami'an kasar ta Syrian domin tattauna wasu muhimman batutuwa da suka hada da fadada shirin soji da kuma hadin gwiwa a bangaren tabbatar da tsaro.
A lokacin tattaunawar, Assad ya soki lamirin manufofin gwamnatin Amurka da kawayenta, ya bayyana cewa, Amurka tana son tsawaita yakin Syria ta hanyar taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma tsarin da take amfani da shi na yiwa Syriar barazana.