Jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Muhammed Suleiman, ya shedawa 'yan jaridu cewa, gonaki masu yawa ne ambaliyar ruwan ta lalata a jihar wanda ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya ne ya haddasa ambaliyar.
A cewar Suleiman, al'ummomi masu yawa daga kananan hukumomi 9 ne ke zaune a kusa da gabar kogin Benue, wanda shi ne kogi na biyu mafi girma a Najeriya, inda kuma a can ne ambaliyar ruwan ta shafa.
A halin yanzu fiye da rabin jama'ar jihar na fuskantar barazanar yiwuwar ambaliyar ruwa.
Mazauna yankin sun tafka hasarar daruruwan dabbobinsu kamar shanu, a sanadiyyar ibtila'in.
Jami'in ya ce, hasarar da ake samu tana kara kamari, kuma ambaliyar ruwan ta zama wani babban kalubale wanda ke yin barazana ga harkokin noma a jihar dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. (Ahmad)