in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bada gargadi game da ambaliyar ruwa
2018-09-15 15:32:16 cri

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta umarci dukkan cibiyoyinta a dukkan fadin kasar da su zauna cikin shirin ko ta kwana sakamakon yawaitar ruwa a kasar.

Mustapha Maihaja, babban daraktan hukumar NEMA ya ce, ana cigaba da samun yawaitar ruwa a kasar ne a sanadiyyar mamakon ruwan sama a sassan kasar.

Ya ce NEMA ta bayyana wasu jihohi 12 a matsayin wuraren da ake sa ran yiwuwar za su fuskanci ambaliyar ruwa a cikin wannan shekarar, ya kara da cewa, ambaliyar ruwan za ta iya faruwa a ko wane lokaci daga yanzu a wadannan jihojin.

Haka zalika, jami'an 'yan sanda a jihar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin kasar sun shawarci mutanen dake zaune a gabar teku da su hanzarta yin kaura kafin ranar Asabar domin kaucewa fuskantar ambaliyar ruwa.

Habibu Musa, kakakin hukumar 'yan sanda ya ce, wannan kira ya zama tilas kasancewar Jamhuriyar Kamaru dake makwabtaka da jihar za ta saki ruwa tekun Lagdo wanda ya yi matukar tumbatsa.

A halin da ake ciki, mutanen da suka mutu a arewacin Najeriya a sanadiyyar ambaliyar ruwa ya kai 53 a cikin watanni 4 da suka gabata, yayin da wasu mutanen 30 suka bace ba'a same su ba, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta sanar a jiya Jumma'a.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China