in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta tura mutanen da gobarar gas ta shafa zuwa ketare don duba lafiyarsu
2018-09-15 15:46:00 cri

Jihar Nasarawa dake tsakiyar Najeriya ta kammala shirye shiryen da suka dace domin fitar da mutanen da suka gamu da gobara a tashar samar da iskar gas zuwa kasar Afrika ta kudu domin duba lafiyarsu.

Gwamna Umaru Al-Makura shi ne ya tabbatar da hakan a Lafia, babban birnin jihar, ya ce 11 daga cikin mutane 36 da hadarin ya rutsa da su sun rasu, kana 8 daga cikinsu suna cikin matsanancin hali.

Ya ce mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya shafa ana duba lafiyarsu ne a cibiyar duba masu fama da annoba dake Abuja, babban birnin kasar.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnati ta kuduri aniyar tabbatar da ganin an ba su kulawar kiwon lafiya mafi inganci.

A ranar Litinin ne dai wata tashar samar da iskar gas dake Lafia ta kama da wuta a lokacin da wata tankar takon mai take ledin gas, bayan da aka samu fashewar bututun gas din wuta ta kama.

Dogara Dalhatu, babban jami'in hukumar kashe gobara na jihar Nasarawa, ya danganta tashin gobarar da tartsatsin wutar lantarki da aka samu a kusa da wajen da lamarin ya auku.

Ababen hawa masu yawa da suka hada da babura da babura masu kafa uku gobarar ta barnata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China