in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar kudin Najeriya ta sauka daga mukamin ta sakamakon zargin ta da aka yi da amfani da takardar bogi
2018-09-15 15:53:23 cri

Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta sauka daga mukamin ta, bayan da aka zarge ta da yin amfani da takardar kammala yiwa kasa hidima ko NYSC ta bogi.

Adeosun wadda ta bayyana kaduwa da zargin da aka yi mata, ta ce ta yanke shawarar sauka daga mukamakin nata ne, domin kare martabar gwamnatin kasar mai ci.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriyar ta fitar game da haka, ta ce fadar shugaban kasa ta amince da murabus din ministar a ranar Jumma'a.

Tuni kuma shugaba Buhari ya amince da nadin karamar ministan kasafin kudi da tsare-tsare Zainab Ahmed, a matsayin mai rikon kwaryar ma'aikatar kudin. Za kuma ta fara aiki tun daga jiya Jumma'a.

A watan Yulin da ya gabata ne dai wasu jaridun Najeriya suka fara yayata batun zargin ministar, suna masu cewa ta karbi takardar NYSC ta bogi, wadda take aiki da ita, lamarin da ya sabawa doka.

Wajibi ne dai dukkanin wanda ya kammala karatu a jami'a, ko manyan kwalejojin ilimi a Najeriya ya yi aikin hidimar kasa na NYSC tsawon shekara guda, kafin fara neman aiki a sassan hukumomin gwamnati.

An nada Adeosun mukamin minista a ma'aikatar kudin Najeriya a watan Nuwambar shekarar 2015, tana kuma daga cikin ministocin gwamnatin Najeriya da ake ganin suna da kwarewar aiki.

A watan Yulin da ya shude, ana tsaka da batun takardar ta bogi, aka zabe ta a matsayin jagorar hukumar zartaswar bankin shige da fice na nahiyar Afirka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China