in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin a ofishin MDD ya bayyana yaki da fatara a matsayin daya daga matakan kare hakkin bil Adama
2018-09-15 16:21:40 cri

Jagoran tawagar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Yu Jianhua, ya ce yaki da fatara daya ne daga muhimman ginshikai, na samar da rayuwa dake cike da walwala ga al'umma, kana hakan na da muhimmanci wajen bunkasuwa, da kare hakkokin bil Adama.

Yu Jianhua, ya bayyana hakan ne a jiya Jumma'a, cikin wani jawabi da ya gabatar yayin taro na 39, na majalissar kare hakkokin bil Adama ta MDD dake gudana yanzu haka. Ya yi tsokacin ne a madadin wasu kungiyoyin yankuna, ciki hadda na kasashe 'yan ba ruwan mu, da na kasar Rasha, da kuma na Sudan ta kudu.

Yu ya ce a yanzu haka, akwai kusan mutane miliyan 800 a sassan duniya daban daban, wadanda ke rayuwa cikin talauci, kuma ayyukan yaki da fatara na duniya na ci gaba da zama masu wahalar sha'ani, inda aka shafe tsawon lokaci ana fama da su.

Ya ce idan har ana fatan kau da fatara, a kuma samar da kyakkyawan yanayin kare hakkokin bil Adama, to ya zama wajibi kasashen duniya su yi aiki tare wajen cimma muradun ci gaba.

A ta bakin Yu, yana da muhimmanci kasashe daban daban, su maida hankali matuka wajen aiwatar da manufofin saukaka da kakkabe talauci, su kuma karkatar da alakar manufofin su ga yanayi na hakika da al'ummun kasashen su mafiya fama da talauci ke ciki.

Daga nan sai ya yi karin haske game da muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa, yana mai cewa yana da kyau kasashen duniya su fadada bude kofa a fannin tattalin arziki, da inganta tsarin hada hadar cinikayya na kasashe daban daban, su kuma gina wani hadin gwiwa na cin moriyar juna, wanda zai yaki fatara a matakan kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China