Sanarwar ta kara da cewa, Yusuf Magaji Bichi ya yi aiki a sassan hukumar DSS daban daban, ya kuma rike mukamai a fannonin tattara bayanan sirri, da na gudanar da bincike, da warware rikici, da kaucewa fadawa hadurra, da na yaki da ta'addanci, da na ba da kariya, da kuma na kula da ma'aikata. Kafin nadin na sa, ya rike mukamin daraktan hukumar a wasu jahohin Najeriya.
A ranar 7 ga watan Agusta ne gwamnatin Najeriya ta sauke Lawal Musa Daura daga mukamin shugabancin hukumar ta DSS, sakamakon zargin sa da aka yi da tura jami'an hukumarsa zuwa harabar majalissar dokokin kasar, inda suka kewaye majalissar tare da hana 'yan majalissar shiga. (Saminu)