Hukumar bada agajin gaggawa reshen jihar Nassarawa ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa, hadarin ya faru ne sakamakon yoyon man fetur, kana ta ce, galibin wadanda suka mutu mutane ne da suka zo kashe kwarkwatan ido. Bayan da wutar ta watsu zuwa babbar hanyar mota da ta nufi Abuja, fadar mulkin kasar, akwai motoci da babura da dama wadanda suka kone su kurmus.
A yau ne kuma, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar da wata sanarwa, inda ya nuna damuwa sosai kan babbar hasarar da aka yi, ya kuma yi kira ga mahukuntar wurin da su tabbatar da samar da duk wata kulawa da ta kamata ga mutanen da suka ji rauni.(Murtala Zhang)