in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutum 1000 ambaliyar ruwa ta raba da mahallan su a jihar Naija
2018-09-13 10:26:49 cri
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Naija dake tsakiyar Najeriya, ta ce mutane 1,300 sun rasa gidajen su, sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Laraba, a wasu unguwanni 8 dake gabashin jihar.

Unguwannin da wannan ibtila'i ya shafa dai na daura ne da madatsar ruwa dake samar da lantarki ta Zungeru, wadda ta tumbatsa bayan da aka sako ruwa daga madatsar ruwa ta Shiroro.

Da yake yi wa manema labarai karin haske game da lamarin a birnin Minna fadar mulkin jihar ta Naija, babban daraktan hukumar ta NSEMA Ibrahim Inga, ya ce al'ummun da lamarin ya shafa sun rasa gidajen su, da kuma gonaki.

Jami'in ya ce an tsugunar da mutanen a wata makarantar firamare dake yankin. Ana kuma tattara bayanai game da yanayin da suke ciki, tare da gudanar da binciken lafiya domin kaucewa barkewar cututtuka.

A wani ci gaban kuma, rundunar sojojin sama ta Najeriya NAF, ta sha alwashin hada gwiwa da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA, wajen shawo kan kalubalen da ambaliyar ruwa ke haifarwa a sassan kasar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China