in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta dauki matakan kaucewa ambaliyar ruwa
2016-05-24 08:56:12 cri

Ministar ma'aikatar muhalli a Najeriya Amina Muhammed, ta bayyana aniyar gwamnatin kasar, don gane da daukar wasu sabbin matakai, na kawo karshen ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a sassan kasar.

Ministar wadda ta bayyana hakan yayin wani taron ganawa da manema labarai a Abuja, fadar mulkin Najeriyar, ta kara da cewa, manufofin za su shafi tsare-tsaren inganta amfani da filaye, da na kaucewa zaftarewar kasa, matakan da rashin su ne ke haifar da ambaliyar ruwa.

Ta kuma ce, akwai wani shiri na kawo karshen rashin makewayi dake shafar yankunan karkara nan da shekara ta 2019, duka dai da nufin tabbatar da ingantaccen muhallin rayuwa ga 'yan Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China