in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanni 64 a Nijeriya
2018-09-07 09:11:40 cri
A kalla unguwanni 64 ne ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Kogi dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya daga ranar 3 zuwa 4 ga wannan watan.

Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar James Ahmadu, ya ce sama da gidaje 150 ne ambaliyar ta shafa a yankin Koton Karfe dake jihar, inda ya ce an kafa sansanoni 5 na wucin gadi ga wadanda ambaliyar ta rutsa da su.

A cewar James Ahmadu, wannan iftila'i ne daga Allah, amma hukumarsa za ta yi bakin kokarinta na ganin ta tunkare ta da cikin gaggawa, domin tabbatar da ceto wadanda ta rutsa da su.

Ya ce an bukaci mutanen da ke zaune a wuraren dake fuskantar barazanar ambaliya su kaura.

A makon da ya gabata ne hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar ta fitar da gargadin aukuwar ambaliyar a jihar Kogi da wasu jihohi 6 dake fadin kasar, tana mai dogaro da yuwuwar karuwar ruwan sama.

A kalla mayan madatsun ruwa 3 ne suka fara sakin ruwa saboda karuwar ruwan dake kwarara Nigeria daga kogin Niger. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China