Rahoton ya kuma bayyana cewa, an fi fama da bala'in ambaliyar ruwa a babban birnin kasar, watau Niamey, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a birnin tun daga daren ranar 13 ga wata zuwa ranar 14 ga wata. Ya zuwa yanzu, bala'in ya riga ya barnata gonaki da dama, kana ya karya wasu gadoji da hanyoyi da ababen more rayuwa da dama.
Haka kuma, Gidan Talebijin din kasar ta Nijer ya daina watsa shirye shiryensa sakamakon ruwan wanda ya shiga babban ginin ofishin Gidan talabijin din.
Bisa kididdigar da ofishin kula da harkokin jin kai na MDD dake kasar Nijer ya fidda a ranar 14, an ce, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa rasuwar mutane 11, ciki har da yara kanana guda 9.
Ministan kula da harkokin jin kai da warware matsalolin da bala'un suka haifa na Nijer Magaji Laouan, ya bayyana cewa, bala'in ambaliyar ruwan ya riga ya rushe gidaje a kalla guda 694, kuma kimanin mutane 4800 ne wannan ibtila'in ya shafa a halin yanzu. Haka kuma, domin fuskantar ibtila'in, gwamnatin jamhuriyar Nijer tana gaggauta ayyukan samar da abinci da kayayyakin agaji ga al'ummomi masu fama da bala'in. (Maryam)