Mukaddashin jakadan kasar Sin dake Najeriya Lin Jing, da babbar sakatariyar ma'aikatar yada labarai da al'adu ta Najeriya Madam Grace Isu Gekpe, da babban jami'in kula da harkokin al'adu na kasar Sin dake Najeriya Li Xuda, da wakiliyar shugaban kwamitin sa ido kan harkokin fina-finai na Najeriya Fatima Abdulkadir, na daga cikin manyan jami'an da suka halarci bikin.
Da yake jawabi, mukaddashin jakadan kasar Sin dake Najeriya Lin Jing ya ce, taron kolin dandalin tattuana hadin-gwiwar Sin da Afirka da aka yi a Beijing kwanan nan, ya samu manyan nasarori da dama, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarta, tare da yin shawarwari da shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang. A halin yanzu Sin da Najeriya na kara yin mu'amalar al'adu tsakaninsu, kuma kasar Sin za ta bude kasuwarta ga fina-finan Nollywood na Najeriya.
A nata bangaren, babbar sakatariyar ma'aikatar yada labarai da al'adu ta Najeriya Madam Grace Isu Gekpe cewa ta yi, bikin nuna fina-finan kasar Sin a Najeriya zai kara fadakar da jama'ar Najeriya kan nagartattun al'adun kasar Sin.(Murtala Zhang)