in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Ba za a dage babban zabe ba
2018-09-13 09:16:10 cri
Kakakin hukumar zabe mai zaman kan ta a Najeriya Rotimi Oyekanmi, ya musanta rade radin da wasu ke yadawa, cewa akwai yiwuwar dage babban zaben kasar na watan Fabarairun shekara mai zuwa.

Cikin wata sanarwa wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, Rotimi Oyekanmi, ya ce wajibi ne su yi tsokaci game da wannan al'amari, ganin yadda wasu kafafen watsa labarai suka fara yada wannan batu maras ma'ana.

Ya ce batun da ake yadawa, ya sabawa kalaman da shugaban hukumar zaben kasar INEC farfesa Mahmood Yakubu ya yi, yayin wani taron tattaunawa na kwamitin hadakar hukumomin dake da ruwa da tsaki a fannin zabe, inda aka tattauna game da batun tsaro yayin zabukan dake tafe, taron da ya gudana a Abuja fadar mulkin kasar.

Oyekanmi ya kara da cewa, a yayin zaman tattaunawar, fasfesa Yakubu ya shaidawa jagororin hukumomin tsaron cewa, yana da muhimmanci su rika ganawa da juna a kai a kai, yayin da babban zaben kasar na badi ke karatowa. Ya kuma bayyana wannan shawara ne domin za ta taimaka, wajen kara nazartar halin da ake ciki a fannin tsaro, ta yadda za a iya kandagarkin duk wani kalubale, da kaucewa tashin hankali kafin, da a lokacin, da ma bayan kammalar zaben. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China