in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun mutu kana 4 sun jikkata sanadiyyar ruftawar gini a Kano dake Najeriya
2018-09-07 09:17:32 cri
An tabbatar da mutuwar mutane 2 kana wasu mutanen 4 suna karkashin kulawar likitoci bayan da wani gini ya rufta a kansu a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, in ji jami'an aikin ceto.

Ginin dai ya rufta ne da yammacin ranar Laraba a yankin Gwammaja dake karamar hukumar Dala a jihar Kano, wanda ita ce cibiyar kasuwanci dake arewacin Najeriya, kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Saidu Mohammed, wadda hukumar tabi sahun jami'an aikin ceton ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mohammed ya ce, wadanda aka yi nasarar ceto su a raye suna cikin matsanancin hali a asibiti.

Ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa har yanzu ba'a tabbatar da musabbabin hadarin ba, amma wata majiyar jami'an ta ce tuni aka fara gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa rushewar ginin.

Hukumar hasashen yanayin ruwan sama ta Najeriya ta yi hasashen yiwuwar samun mamakon ruwan sama a kasar a bana, inda ta gargadi mutanen dake zaune a tsoffin gidaje da su hanzarta gyara gidajensu domin kaucewa rushewar gidajen. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China