Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta ce sashen ma'aikatar mai bada taimakon yaki da ta'addanci (ATA) ne ya samar da kudi tare da ginawa da kuma samar da kayayyakin aiki ga sabuwar cibiyar bada horon.
Sabuwar cibiyar ita ce irinta ta farko da sashen na ATA ya taba ginawa a yankin Afrika ta yamma. Idan ta fara aiki, ana sa ran za ta fada ayyukan ATA zuwa horar da jami'an kasar Senegal da na sauran wasu kasasehn yammacin Afrika abokan hulda.
Cibiyar za ta samar da horo kan muhimman dabaru da suka hada da matakan tunkarar rikici da na ababen fashewa, da yadda za a gudanar da bincike bayan tashin ababen fashewa da kuma ayyukan sintiri a kan iyakoki. (Fa'iza Mustapha)