in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane 4 da kamfanoni 5 bisa zarginsu da taimakawa Syria
2018-09-07 10:05:15 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta sanya takunkumin kudi kan wasu mutane 4 da kamfanoni 5, tana mai zarginsu da taimakawa wajen samar da makamai ko kuma tura man fetur ko samar da taimakon kudi ko na kayayyaki ga gwamnatin Assad ta Syria.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce mutanen da aka sanyawa takunkumin 'yan kasar Syria ne da Lebanon, sauran kuma kamfanoni ne dake Syria da Lebanon da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ta kara da cewa, takunkuman na nuni da cewa, Amurka za ta ci gaba da daukar kwararan matakan tilasta yanke duk wani taimako ga gwamnatin Assad da maso goya mata baya. Haka kuma, za ta ci gaba da amfani da duk wani mataki dake akwai, na mayar da gwamnatin Assad saniyar ware. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China