in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon hayan shawarwari tsakanin DPRK da Amurka
2018-09-11 21:17:37 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan tattaunawa da sasantawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin tana maraba da yin tattaunawa tsakanin kasashen biyu, kuma hakan zai ci gaba da sassauta halin da ake ciki kuma ci gaba da tattaunawar zaman lafiya game da zirin Koriya ya dace da muradun dukkan bangarorin da abin ya shafa da ma abin da duniya ke fatan gani.

Hakan dai na zuwa ne bayan da fadar shugaban Amurka ta White House ta sanar a jiya Litinin cewa, ta samu wasika daga shugaba Kim Jong Un na Koriya ta arewa game da bukatar yin wata ganawa da shugaba Donald Trump na Amurka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China