Sharhin ya ce, idan har ana bukatar kawar da rashin amincewa da juna tsakanin kasashen biyu, ya kamata Koriya ta Arewa da Amurka su fahimci juna su kuma girmama juna, da nuna sahihanci ga juna kana su hada kai.
Haka kuma don ganin an kyautata dangantakar dake tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, Koriya ta Arewa ta nuna sahihanci ta hanyar daina yin amfani da filin gwajin makaman nukiliya dake arewacin kasar da mikawa Amurka gawawwakin sojojin kasar. Amma kasar Amurka ta bayyana cewa, za ta kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, amma ba ta dauki matakai ba, har ma ta gudanar da abubuwan da suka saba hakan.
Sharhin ya yi nuni da cewa, kasar Koriya ta Arewa ta maida matsalolin da ake fuskanta na wani lokaci a kokarin kyautata dangantakar dake tsakaninta da Amurka don cimma buri daya tare, akwai bukatar Amurka ta kawar da takunkumin da ta kakaba mata da nuna imani da girmama Koriya ta Arewa don kyautata dangantakar dake tsakaninsu. (Zainab)