in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan kasashe biyu na zirin Koriya za su kyautata hulda tsakaninsu
2018-08-22 20:17:08 cri

Yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin, za ta ci gaba da goyon bayan yunkurin kara kyautata huldar dake tsakanin kasashe biyu na zirin Koriya, wato Koriya ta Arewa da ta Kudu, tare da sauran kasashen duniya.

Kafin wannan, ministan tsaron Koriya ta Kudu ya bayyana cewa, kasarsa da kasar ta Koriya ta Arewa, sun riga sun daddale yarjejeniya game da soke tashoshin sa ido sama da goma da aka gina a wuraren da ba na aikin soja ba, ta yadda sassan biyu za su kara inganta fahimtar juna dake tsakaninsu. Haka kuma za su kara soke irin wadannan tashoshi na sa ido a nan gaba.

Lu Kang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana farin ciki da ganin kasashen biyu sun cimma matsaya guda, tare kuma da samun sabon ci gaba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China