in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Micheal Kersey: "Ana iya baya da mota don a ceci kare?"
2018-08-29 19:59:40 cri
"Idan an yi imani kan cewar matakin kara harajin kan kayayyakin yanke ciyayi zai taimaka wajen samar da guraben aikin yi a Amurka, to, kamar an amince ne cewa, idan aka yi baya da mota, za a iya ceton karen da motarka ta taka." Wannan shi ne kalaman da Micheal Kersey, shugaban wani kamfani mai samar da na'urorin yanke ciyayi na kasar Amukra, ya yi a ranar 22 ga wata yayin wani taron sauraron ra'ayin jama'a kan manufar kara haraji kan kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 200 da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasar Amurka da gwamnatin kasar Amurka ke shirin dauka.

Hakika kalaman Mista Kersey sun nuna ra'ayin yawancin masu halartar taron, wadanda ke bukatar gwamnatin Amurka da ta yi taka tsan-tsan, tare da la'akari da muradun jama'a da kamfanonin kasar yayin da take tsara manufofinta. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China