in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takunkumin da Amurka ta sanya wa Iran ya bata ran kungiyar Turai
2018-08-27 19:47:39 cri
Huldar dake tsakanin kasar Amurka da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU tana fuskantar canje-canje. A karshen watan Yulin bana ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump da shugaban kungiyar tarayyar kasashen Turai Jean-Claude Juncker suka sanar da cewa, dangantakar abokantaka dake tsakanin bangarorin biyu ta shiga sabon matsayi mai kyau. Sa'an nan, a watan nan da muke ciki, bangarorin biyu sun fara zargin juna, lamarin da ya sa dangantakar dake tsakaninsu ta yi tsami. Kuma, babban dalilin da ya sa hakan, shi ne, takunkumin da kasar Amurka ta sanya wa kasar Iran.

Da yake tsokaci kan zargin da kasar Amurka ta yi wa kasashen Turai, shugaban majalisar zartaswar kungiyar EU Donald Tusk ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta girmama kawanyenta, sabo da ba su da yawa a halin yanzu. (Maryam) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China