in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da ministan harkokin wajen Rasha
2018-04-23 20:50:43 cri
Yau Litinin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing.

Xi Jinping ya ce, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyara kasar Sin a watan Yunin wannan shekara, inda kuma zai halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da za a yi a birnin Qingdao. Shugaba Xi yana sa ran ganawa da shugaba Putin domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yin hadin gwiwa da sauran mambobin kungiyar domin neman ci gaban kungiyar a nan gaba.

A nasa bangare, Sergei Lavrov ya ce, Sin da Rasha suna mutunta dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD, kuma dukkansu suna son karfafa hadin gwiwarsu bisa tsarin hadin gwiwar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China