Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, wannan ziyara ta shaida matsayin musamman, game da dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Hua ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau 26 ga wata cewa, Vladimir Putin ya sake zama shugaban kasar Rasha, ana kuma fuskantar sabuwar damar bunkasuwa a tsakanin Sin da Rasha, a wannan gaba ne Wang Yi zai gana da shugabannin kasar Rasha, kana zai yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergej Lavrov, inda za su yi musayar ra'ayoyi kan ganawar da ta wakana tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, da sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a manyan fannoni da sauransu. (Zainab)