Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya aike wa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sakon taya murnar zama shugaban kasar Sin a karo na biyu.
A cikin sakon da ya aike a yau Asabar, Putin ya ce ya yi ammana cewa, bisa kokarin da kasashen 2 suke yi, tabbas ne za su kara inganta huldar kawance da taimakawa juna a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Lamarin da ya ce zai kara samar da alheri ga jama'ar kasashen 2, da azama kan samun tsaro da kwanciyar hankali a nahiyoyin Turai da Asiya da ma duniya baki daya. (Tasallah Yuan)