in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ramaphosa: Kasashen Afrika sun yi maraba da dangantakar moriya tsakaninsu da Sin
2018-09-07 10:10:30 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya fada a jiya Alhamis cewa kasashen Afrika sun yi maraba da dangantakar moriyar juna tsakaninsu da kasar Sin kuma suna goyon bayan taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashensu.

Da yake jawabi bayan komawarsa gida daga kasar Sin bayan halartar taron kolin (FOCAC) na Beijing 2018 wanda aka kammala a wannan mako, Ramaphosa ya bayyana taron kolin da cewa babbar nasara ce.

Ya ce kasashen Afrika da dama sun gamsu cewa kasar Sin babbar aminiya ce gare su wadda take burin kyautata huldarta da su domin cimma nasarar samun bunkasuwa ta fuskar ci gaban masana'antu.

Ramaphosa ya ce kasashen Afrika suna burin samun ci gaban ta hanyar bunkasar masana'antu, ya kara da cewa, kasashen Afrika da Sin suna son cimma nasarar samar da daidaito a harkokin cinikayya a tsakaninsu.

Ya ce kasar Afrika ta kudu da kasar Sin sun kulla yarjejeniyoyi masu yawa a lokacin wannan ziyarar tasa.

Yarjejeniyoyin za su share fagen samun bunkasuwar tattalin arziki, da ci gaban ilmi, da samar da damammakin guraben ayyukan yi ga kasar Afrika ta kudu, in ji Ramaphosa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China