Jami'in wanda ya bayyana hakan cikin wata zantawar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce alakar sassan biyu, dangantaka ce ta moriyar juna ba wai ga kasar Sin kadai ba har ma ga duniya baki daya.
Onunaiju ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya ta sanya kyakkyawar makoma ga taron na FOCAC, kuma hakan abu ne mai muhimmanci ga nahiyar Afirka. Yanzu haka kasar Sin ta sake sanar da aiwatar da wasu sabbin matakan raya alaka da kasashen Afirka guda 8 wadanda suka hada da fannonin raya masana'antu, da ababan more rayuwa da saukaka harkokin cinikayya da kare muhalli, dukkansu ana fatan aiwatar da su nan da shekaru uku masu zuwa da ma nan gaba.
Ya ce, wadannan sabbin matakai za su taimaka matuka wajen raya nahiyar. Don haka ya shawarci shugabannin kasashen na Afirka da su inganta manufofinsu ta yadda za su ci gajiyar sabbin matakai da shirye-shiryen. (Ibrahim)