in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana: Ya kamata Afrika ta hada gwiwa da Sin don samar da dabarun aiki tare
2018-09-06 10:16:58 cri
Wata kwararriya ta bayyana cewa kamata ya yi kasashen Afrika su kara kada kai domin yin aiki tare da kasar Sin wajen bullo da dabarun samar da kyakkyawar makoma bayan kammala taron kolin Beijing na hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika (FOCAC) wanda aka fitar da wasu tsare tsare da za su kara kyautata hadin gwiwar Sin da Afrika.

Bernadette Deka, babbar daraktar wata cibiyar tsare tsare da yin nazari ta ce shawarar da aka yanke ta kulla alakar shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar raya dawwamamman cigaba na MDD nan da shekarar 2030, da kuma ajandar kungiyar tarayyar Afrika AU nan da shekarar 2063 ya nuna cewa kasashen Afrika suna kan turbar samun hanyar cimma matsaya na duba hanyoyin da za su tabbatar da kawo bunkasuwar cinikayya da tattalin arzikinsu wanda ya dace da yanayinsu.

A cewarta, mu'amala tsakanin mutum da mutum dole ne ta bada fifiko ga matasa, ta kara da cewa, shawarwarin da aka cimma a lokacin taron kolin Beijing sun shafi yadda za'a kara mayar da hankali wajen bullo da wasu cibiyoyin fasahohi da cibiyoyin koyar da sana'oi wadanda za'a kafa su don samar da kwarewa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China