in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda: Wani dan bindiga ya hallaka mutane 2 a jihar Florida ta Amurka
2018-08-27 11:15:00 cri
Wani mahari dauke da bindiga, ya hallaka mutane biyu kafin ya bindige kan sa a wata cibiyar wasannin na'ura mai kwakwalwa dake birnin Jacksonville na arewacin Floridan kasar Amurka.

Wani jam'in 'yan sandan birnin Mike Williams, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, harbe harben sun sabbaba jikkatar karin wasu mutanen 11, ko da yake mutanen ba sa cikin wani mummunan hali.

Ya ce an kai mutane 9 asibiti, ciki hadda wadanda ke dauke da raunukan bindiga. Kaza lika wasu 2 dauke da raunukan harsashi su ma sun kai kan su asibiti.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharin ya bude wuta ne a kusa da wata kasuwa da misalin karfe 1:30 na rana agogon GMT, yayin da ake tsaka da nuna gasar wasannin na'ura mai kwakwalwa kai tsaye ta akwatunan talabijin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China