in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da sojojin Kamaru dubu 1 ne za su shiga shirin MDD a CRA
2018-08-26 16:22:21 cri
Ministan tsaron jamhuriyar Kamaru Joseph Beti Assomo ya sanar a jiya Asabar cewa, Kamaru ta tura sojoji na runduna ta 5 na dakarunta domin su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a makwabciyar kasar wato jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR).

Sojojin za su tallafawa shirin MDD ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a CAR tare da mutunta dokokin MDDr da kare hakkin bil adama a lokacin da suke bakin daga, in ji ministan.

Tagawar wani bangare ne na dakarun gamayyar kasa da kasa na shirin wanzar da zaman lafiya ta MDD dake aiki a jamhuriyar Afrika ta tsakiya (MINUSCA) wadda ta fara aikin tun a shekarar 2014 domin kare fararen hula a CAR karkashin yarjejeniyar MDD.

"Daga cikin jami'an kiyaye zaman lafiya 11,200 dake yiwa MINUSCA aiki, Kamaru ta samar da sama da jami'ai dubu a cikin bataliyar," in ji Assomo.

Kanal Martin Prospere Bayemi, kwamandan runduna ta 5 na dakarun sojojin Kamaru ta ce sun shirya tsab, saboda sun samu dukkan kwarewar da ta dace da tsarin MDD, kuma suna da dukkannin kayan aikin da ake bukata don gudanar da aikin a tawagar ta MINUSCA. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China