in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da kaso daya bisa biyar na al'ummar Kamaru na amfani da miyagun kwayoyi
2018-08-28 10:52:06 cri
Ministan ma'aikatar watsa labarai, kuma kakakin gwamnatin kasar Kamaru Issa Tchiroma, ya ce sama da kaso daya bisa biyar na al'ummar Kamaru na amfani da kwayoyi masu jirkita tunani.

Issa Tchiroma ya bayyanawa wani taron manema labarai a birnin Yaounde cewa, alkaluman sakamakon wani bincike ne da aka gudanar, sun kuma nuna cewa kaso 21 bisa dari na 'yan kasar sun taba shan miyagun kwayoyi, kana kaso 10 bisa dari na ta'ammali da kwayoyin akai akai.

Kaza lika binciken wanda kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi na kasar ya gudanar ya nuna cewa, cikin masu shan miyagun kwayoyi a ko da yaushe, kaso 60 bisa dari na tsakanin shekaru 20 zuwa 25, yayin da yawan yara 'yan kasa da shekaru 15 dake shan kwayoyin masu jirkita kwakwalwa ya kai 12,000.

A cewar ministan, rashin tsaro da ake fama da shi a yankunan dake magana da yaren Turancin Ingilishi a kasar ta Kamaru, na da nasaba da shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa.

Ya ce tashe tashen hankula a yankin, na nuni ga irin mummunan tasirin da miyagun kwayoyi ke yi ga rayuwar matasa. Sai dai a cewar sa, gwamnati na iya kokarin ta wajen ganin ta dakile yaduwar wannan annoba.

Wasu alkaluman kuma sun nuna cewa, yawan jami'an tsaro da suka rasu sakamakon fadace fadace da aka kwashe kusan shekara 1 ana fama da su a yankin sun kai 109. To sai dai kuma gwamnati ba ta fayyace adadin 'yan awaren yankin da suka rasa rayukan su ba.

'Yan awaren dai na fatan kafa kasar Ambazonia, wadda za ta hada yankunan arewa maso yamma, da kudu maso yammacin kasar ta jamhuriyar Kamaru, wadda mafi yawan yankunan ta ke magana da yaran Faransanci. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China