Tun da farko dai mayakan 'yan awaren sun sanar da cewa sun hallaka sojoji 9 ne a lokacin da suka kaddamar da harin, to sai dai kanal Badjeck yace labarin ba gaskiya ba ne.
"Labaran bogi suna cigaba da zagawa a kafafen sadarwa na zamani inda ake cewa an kashe sojoji 9 tare da kwace makamansu wanda mayakan 'yan ta'addan suka yi a yankin Wum. Tabbas, an kaddamar da hari kan bataliyar sojoji ta Zhoa gendarmerie brigade kuma an kashe soji 2 a lokacin harin. Sai dai an fatattaki mayakan 'yan awaren 12 kana wasu da dama sun tsere da raunuka. Sannan an kwace makamansu da alburusai masu yawa" in ji kanal Badjeck.
A cewar gwamnatin kasar, jami'an tsaro 109 ne aka kashe tun bayan da 'yan awaren suka fara kaddamar da hare hare cikin shekara guda a yankin na masu magana da yaren Turanci a kasar Kamaru. Sai dai kawo yanzu ba'a tantance ko dakarun 'yan awaren nawa ne aka hallaka ba.