Ministan ya bayyana hakan ne a wani sansanin dakarun tsaro na gamayyar kasa da kasa a Mora dake yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru, a lokacin da yake ganawa da wasu tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram su 100 da suka aje makamansu.
Ya ce horon da za'a basu zai taimaka musu wajen samun sana'o'in da zasu dogara da kansu.
Paul Atanga Nji yace, shugaba Paul Biya na kasar ya samar da wuraren da za'a horas da matasan inda zasu koyi sana'o'i. Wasu daga cikinsu sun nuna sha'awar koyon aikin noma, da aikin kafinta, da aikin gyaran ababen hawa. Don haka kowane mutum daga cikinsu zai koyi sana'ar da zai iya tsayawa da kafarsa.
A cewar ministan, irin kulawar da aka nunawa tsoffin mayakan 'yan ta'addan ya bayyana a fili irin yadda dakarun sojojin Kamaru ke mutunta hakkin dan adam a wajen tukarar abokan gaba da fursunonin yaki.