in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Sin ya yi alkawarin bada rancen dala miliyan 500 ga Afrika
2018-09-07 09:55:57 cri
Bankin raya ci gaba na kasar Sin (CDB), wanda shi ne babban bankin tsare-tsare na kasar, a ranar Alhamis ya sanya hannu kan yarjejeniyar bada rancen dala miliyan 500 ga bankin shigi da fici na Afrika wato Afreximbank.

An kulla yarjejeniyar ne a lokacin taron dandalin zuba jari da aka gudanar a jiya Alhamis a Changsha, babban birnin lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.

Afreximbank babbar cibiyar hada hadar kudi ne na kasa da kasa wanda ke bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasashen Afrika har ma da wajen Afrika. Bankin zai hada gwiwa da bankin CDB wajen samar da kudaden ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, da lantarki, da sadarwa, da sufuri, da aikin gona a kasashen Afrika, kamar yadda aka bayyana karkashin yarjejeniyar.

Bankin CDB ya kuma sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da gwamnatin lardin Hunan a lokacin taron dandalin da nufin bunkasa jarin da lardin ke da shi a nahiyar Afrika.

A ranar Laraba, CDB ya jagoranci kafa wata cibiyar hadin gwiwar harkokin kudi ta Sin da Afrika tare da wasu cibiyoyin harkokin kudade 16 na Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China