in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Afirka ta Tsakiya
2018-09-06 16:30:57 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta nuna goyon baya da taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya wajen shimfida zaman lafiya da raya kasa, Sin tana son kara yin imani da juna a fannin siyasa tare da kasar Afirka ta Tsakiya, da fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da taimakawa kasar a fannin samar da abinci da inganta rayuwar jama'a, za kuma ta ci gaba da tura tawagar likitoci zuwa kasar Afirka ta Tsakiya.

A nasa bangare, Touadera ya bayyana cewa, kasarsa tana godiya ga kasar Sin bisa ga taimakon da take ba ta wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasar, kana tana son kara yin mu'amala a tsakanin jam'iyyun kasashen biyu da kuma manufofin raya kasa, da hada kai wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninsu, da kara yin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da manyan ayyuka 8 da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron kolin FOCAC na wanna karo da aka kammala a birnin Beijing. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China