in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanr da taron kolin hadin gwiwar hukumomi masu zaman kasu na Sin da Afrika a Zhejiang
2018-09-07 09:24:01 cri

A karon farko an gudanar da taron kolin hadin gwiwar hukumomi masu zaman kansu na Sin da kasashen Afrika a birnin Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin a ranar Alhamis.

Sama da wakilan gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu da ma'aikatu na kasar Sin da kasashen Afrika 300 ne suka halarci taron kolin.

Take taron shi ne "Zurfafa hadin gwiwar hukumomi masu zaman kansu don raya tattalin arzikin Sin da Afrika", an gudanar da taron ne da nufin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da gina wani tsari na yin musaya da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen Afrika, da daga matsayin kyakkyawar hadin gwiwa, da kyautata dangantaka da samar da moriyar juna da kuma gina dangantaka mai karfi tsakanin al'ummomin Sin da Afrika a nan gaba.

"Kamfanoni masu zaman kansu za su iya samun kwarin gwiwa wajen bunkasa tattalin arziki, da kyautata hulda, da samar da damammaki na guraben ayyukan yi da kuma cimma nasara tare," in ji shugaban kasar Senegal Macky Sall.

Ya bada shawarar cewa, kamata ya yi kasar Sin da kasashen Afrika su saukaka matakan da ake bi wajen zuba jari, su samar da yanayin kasuwanci mai kyau, su karfafa hulda a tsakanin kamfanoni masu zaman kansu na Sin da Afrika, kana a baiwa kamfanonin kasar Sin kwarin gwiwa don bada gudunmawa wajen tafiyar da harkokin kamfanonin kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China