in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa sun yabawa sakamakon da aka samu a taron kolin Beijing na FOCAC
2018-09-06 11:24:43 cri

Tun daga ranar 3 zuwa 4 ga wata, an gudanar da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC cikin nasara. Kasa da kasa sun maida hankali kan taron kolin, a ganinsu, an samu kyakkyawan sakamako a gun taron, wanda ya inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da aza tubali ga hadin gwiwarsu a sabon zamani.

A cikin jawabin da ya bayar a gun bikin bude taron kolin Beijing na FOCAC a ranar 3 ga wata, shugaba Xi Jinping ya sanar da manufofin Sin biyar wato kaucewa tsoma baki kan hanyar raya kasashen Afirka mai dacewa da su, da rashin tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashen Afirka, da kaucewa tilasta sauran kasashe bisa ra'ayin Sin, da kaucewa gindaya sharruda yayin da ake samar da gudummawa ga Afirka, da kuma kaucewa samun moriya a fannin siyasa daga aikin zuba jari da tattara kudi a Afirka.

Bangarori daban daban sun nuna amincewa ga manufofin.

Mashahurin masanin tattalin arziki na kasar Afirka ta Kudu Mundie ya bayyana cewa, Afirka da Sin sun sada zumunta da kuma yin hadin gwiwa a dogon lokaci. A ganin kasashen Afirka, ana nuna adalci da samun moriyar juna kan hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin. Koda yake a kan samu sauyin yanayin kasa da kasa, ba za a canja tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin ba.

Farfesa a sashen ilmin kasa da muhalli na jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Ilando ya bayyana cewa, manufofin biyar suna da babbar ma'ana kan raya dangantakar dake tskanin Afirka da Sin, wanda ya shaida cewa kasar Sin aminiyar Afirka ce ta gaske.

A gun taron kolin Beijing na FOCAC a wannan karo, shugaba Xi Jinping ya gabatar da manyan ayyuka 8 da za a gudanar a shekaru 3 masu zuwa wato raya masana'antu, raya muhimman ababen more rayuwa, samar da sauki ga cinikayya, samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, kyautata kwarewar gudanar da harkokin kasa, kiwon lafiya, mu'amalar al'adu, da kuma zaman lafiya da tsaro.

Game da wannan, masanin tattalin arzikin kasar Zimbabwe Mousenger ya yi tsammanin cewa, manyan ayyukan 8 muhimmin sakamako ne da aka samu a gun taron kolin, wanda ya nuna kyakkyawar makoma kan hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin a dukkan fannoni a nan gaba. Ya yi imanin cewa, ta hanyar aiwatar da ayyukan yadda ya kamata, za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi.

Mashahurin mai watsa labaru na kasar Nijeriya Enshikri ya bayyana cewa, FOCAC wani muhimmin dandali ne na hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin, aikin sa kaimi ga raya masana'antu dake cikin manyan ayyukan 8 zai kara samar da dama ga ci gaban masana'antun kasashen Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China