in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarun Amurka: yakin ciniki zai haifar da illa matuka ga manoman kasar Amurka
2018-08-26 16:44:42 cri
A yayin da yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar a wurare daban daban na duniya ke kara tsananta, kafofin yada labaru na kasar Amurka sun yi hasashen cewa, dorewar yakin cinikin zai haifar da babbar illa ga manoman kasar.

Bisa hasashen da kafofin watsa labarun kasar Amurka suka yi, sakamakon karin harajin kwastam da ake karba kan wasu amfanin gona, kudin shigar da manoman kasar Amurka za su samu a shekarar 2018 zai zama mafi kankanta cikin shekaru 12 da suka wuce.

An ce kudin shigar da manoman kasar suka samu a shekarar 2013 ya kai dalar Amurka biliyan 123, sai dai a wannan shekara, an kiyasta cewa kudin da za su samu ba zai wuce na dala biliyan 60 ba.

Haka kuma a cewar kafofin yada labarun kasar Amurkar, ko da yake gwamnatin kasar za ta iya bada kudin tallafi ga aikin gona, sa'an nan manoman za su iya kara kokarin fitar da amfanin gona ga wasu kasashe, amma duk da haka, aikin gona da kauyuka na kasar Amurka za su fuskanci babban kalubale. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China