in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bankin AFDB: Kasashen Afirka ba sa fama da rikicin bashi
2018-09-06 10:06:42 cri

Shugaban bankin raya Afirka (AfDB) Akinwumi Adesina, ya karyata zargin da ake cewa, kasashen Afirka na fama da ricikin basussuka. Shugaban ya karyata wannan zargi ne yayin zantawa da manema labarai a gefen taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka kammala a birnin Beijing na kasar Sin.

Adesina ya ce, baki daya a shekarar 2017 da ta gabata bashin da ake bin kasashen nahiyar kaso 37 cikin 100 na alkaluman GPD ne, sabanin kaso 22 cikin 100 a shekarar 2010, kuma wannan ba wata damuwa ba ce ga kasashen da ba sa samun kudaden shiga masu yawa.

Jami'in ya jaddada cewa, alkaluman suna kasa da kaso 100 ko 150 cikin 100 na galibin kasashen dake samun kudaden shiga da dama da kuma sama da kaso 50 cikin 100 na kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa.

Masu fashin baki na ganin cewa, jarin da kasar Sin take zubawa a kasashen Afirka ba za su karawa nahiyar wani nauyin bashi ba. Sai dai ma daga karshe su magance matsalar.

Galibi dai basusukan da kasar Sin ke baiwa kasashen nahiyar, sun fi karkata ne ga gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, daya daga cikin muhimman abubuwan dake kara janyo masu sha'awar zuwa jari daga ketare. Idan kasa tana da kyawawan ababan more rayuwa, masu zuba jari za su yi sha'awar zuwa za kuma su samar da guraben ayyukan yi daga karshe ita ma gwamnati za ta kara samun kudaden shiga. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China