Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba shehu wanda ya sanar da hakan Jumma'ar nan cikin wata sanarwa, ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne zai jagoranci sama da manyan jami'an gwamnatin kasar 20 zuwa kasar Sin don halarta taron na FOCAC da zai gudana a ranar 3 da 4 ga watan Satumba.
Garba shehu ya ce, yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Sin shugaba Buhari zai tattauna kan kudaden samar da ayyukan more rayuwa a Najeriya.
Haka kuma shugaba Buhari zai yi amfani da wannan dama wajen kimanta irin ci gaba da aka samu ya zuwa wannan lokaci kan taimakon da kasar Sin ke baiwa Najeriya a fannin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a kasar, musamman ayyukan gina layin dogo da samar da wutar lantarki dake gudana.(Ibrahim)