in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bayar da gargadi na yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa
2018-09-06 09:50:42 cri
Hukumar hasashen ruwan sama ta Najeriya ta fitar da wani gargadi a jiya Laraba game da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a sakamakon mamakon ruwan sama a fadin kasar.

Mai rikon mukamin daraktan hukumar hasashen ruwan sama ta NIHSA, Ahmed Bashir, ya ce ya zama tilas a yiwa mutane gargadi saboda yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar.

Ya ce watannin uku na shekara da suka kunshi watan Yuli, Augasta da Satumba da ake kira "JAS" su ne lokutan da aka fi samun barazanar ambaliyar ruwa a kasar.

Dama dai hukumar ta sanar da hasashen da ta yi game da ruwan sama na shekarar 2018 inda ta ce, mai yiwuwa ne daga ranar 28 ga watan Satumba ruwan sama zai dauke a jahohin Sokoto da Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ya ce watan Disamba shi ne lokacin da ruwan saman zai tsaya a yankunan kudancin kasar dake gabar teku.

Bashar ya ce ambaliyar ruwa da tumbatsar kogin Niger zai ci gaba da karuwa, don haka aka gargadi al'umma da su yi kaffa-kaffa don kaucewa fuskantar mummunar hasara.

Ya kara da cewa hasashen da aka yi na yiwuwar fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a jahohin Kebbi, Niger, Kwara, Kogi, Edo, Anambra, Delta, Rivers da Bayelsa yana nan bai sauya ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China