in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 11 a sanadiyyar hari a tsakiyar Najeriya
2018-09-04 09:22:26 cri
Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 11 da kuma jikkata wasu mutanen 12 a sanadiyyar wani hari da aka kaddamar a birnin Jos dake shiyyar tsakiyar Najeriya.

Kakakin hukumar 'yan sandan yankin Terna Tyopev, ya ce ba'a tabbatar da dalilin kaddamar da harin na jahar ta Plateau ba.

Tyopev ya ce, an kai harin ne a yankin Lopandet Dwei Du dake cikin birnin kuma an yi ta harbin kan mai tsautsayi ne kan mazauna yankin.

Tuni dai aka garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti don ba su kulawa.

Kakakin 'yan sandan ya ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda ke da hannu wajen kaddamar da harin.

A ranar Larabar data gabata ma, mutane 8 aka kashe a sanadiyyar wani harin da aka kaddamar kan wasu da ake zargin barayin shanu ne a wani yankin na daban dake jahar ta Plateau. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China