in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce IS ta shiga sansanonin 'yan gudun hijira
2018-09-06 09:17:31 cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce, kungiyar IS tana gudanar da ayyukanta a wasu sansanonin 'yan gudun hijira dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar da ta yi fama da tashin hankalin Boko Haram.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar Ahmed Bello wanda ya sanar da hakan yayin da yake yiwa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar karin haske game da yanayin tsaro a wani taron game da yanayin jin kai da ci gaban da aka samu, ya ce rundunarsa ta gano cewa, uku daga cikin mayakan Boko Haram 22 da aka kama watanni biyun da suka gabata, mambobin IS ne。

Ya ce, galibi 'yan ta'addan na taruwa ne a sansanin 'yan gudun hijira domin su tayar da hargitsi ba tare da an gano su ba. Yana mai cewa, damke 'yan ta'addan ya sa an samu raguwar tashin bama-bamai a birnin Maiduguri.

A watan Yuni ne, kafofin watsa labarai a kasar suka ba da rahoton cewa, kasar dake yammacin Afirka na fuskantar barazana daga kungiyar IS, amma hukumomin tsaro suka karyata rahoton cewa, kasar ba ta fuskantar wata barazana daga wasu kungiyoyin 'yan ta'adda na gida ko ketare ba. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China