A ranar Alhamis din da ta gabata ne, Bukola Saraki, wanda mukaminsa ke a matsayi na 3 a jerin mukaman shugabancin Najeriyar, ya tabbatar da zai shiga a fafata da shi a neman wanda jam'iyyarsa ta PDP za ta tsayar takarar shugabancin Najeriya.
Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taro da ya gudanar a Abuja fadar mulkin kasar, shugaban majalissar dattawan ya ce, yana da dukkanin abun da ake bukata na gogewa domin ciyar da Najeriya gaba.
A ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata, Saraki ya sauya sheka daga jami'iyyar APC mai mulki zuwa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP, lamarin da ta haifar da cece kuce a tsakanin magoya baya na jam'iyyun biyu.
Bayan komawar tasa PDP ne kuma, jagororin jam'iyyar suka ayyana shi a matsayin uban jam'iyyar na kasa. Kafin nan, shugaban majalissar dattawan ya taba bayyana aniyarsa ta fafatawa da shugaban kasar mai ci wato Muhammadu Buhari, a zaben watan Fabarairun shekarar 2019 dake tafe. Sauran manyan 'yan siyasar dake neman shugabancin Najeriyar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar. (Saminu)