in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya bayyana rashin tabbas game da yanayin Libya
2018-09-06 11:06:22 cri
Babban wakilin shirin wanzar da zaman lafiyar MDD a kasar Libya (UNSMIL) Ghassan Salame ya sanar a jiya Laraba cewa, yanayin da ake ciki a Libya akwai rashin tabbas, a jawabinsa na farko ga kwamitin sulhun MDD bayan tattaunawa ta baya bayan nan game da rikicin kasar Libya wanda aka gudanar a watan Augasta.

Salame, wanda kuma shi ne babban wakilin sakatare janar na MDD a Libya, ya bayyana tashin hankalin da ya barke a Tripoli wanda ya fara tun daga ranar 26 ga watan Augasta a matsayin abin ta da hankali bayan da tashin hankalin ya dan lafa a watan Mayun 2017, an tura manyan tankokin yaki da makaman artillery zuwa yankunan lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane 61 da jikkata wasu 159.

Kana ya bayyana fargaba cewa kasar Libya za ta iya zama wata matattarar 'yan ta'adda, wanda ta kunshi mayakan IS, don haka ya bukaci kwamitin sulhun MDD da ya kara bada taimako don shawo kan barazanar da ake fuskanta.

Bugu da kari, wakilin MDDr ya bayyana yakin da ake fafatawa tsakanin gwamnatin kasar Chadi da 'yan tawaye da na kudancin Libya, inda ya bayyana cewa akwai bukatar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Chad, Sudan, Niger da Libya tana bukatar a gaggauta aiwatar da ita, domin ganin cewa Libya ba ta kasance a matsayin wata tungar mayaka ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China