in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ahunna Eziakonwa: Shawarar ziri daya da hanya daya za ta rage tsadar cinikayya tsakanin Sin da Afirka
2018-08-31 11:22:52 cri
An bayyana shawarar nan ta ziri daya da hanya daya da Sin ta gabatar, a matsayin dabara da muddin aka aiwatar da ita yadda ya kamata, za ta iya rage tsadar gudanar da hada hadar kasuwanci tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, baya ga karfafa alakar sassan da shawarar za ta yi.

Mataimakiyar darakta, wadda kuma ke jagorantar sashen Afirka a shirin samar da ci gaba na MDD ko UNDP a takaice Ahunna Eziakonwa, ita ce ta bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ahunna Eziakonwa ta ce Sin da nahiyar Afirka, na da dadadden tarihi a fannin hadin gwiwar ci gaba, matakin da ya samu fadada matuka cikin shekaru goma da suka gabata. Ta ce cinikayya, da zuba jari na kai tsaye, tare da lamuni da Sin ke samarwa ga Afirka, su ma sun kara yawaita yadda ya kamata.

Ta ce Sin na da kaso 25 bisa dari na jimillar sassan kasuwancin da Afirka ke yi da bangarorin duniya a shekarar 2015. Kana yawan darajar kayan da kasashen nahiyar Afirka ke fitarwa zuwa Sin, sun daga daga kasa da dalar Amurka biliyan 20 a shekarar ta 2005, zuwa dalar Amurka biliyan 110 a shekarar 2014. Ahunna Eziakonwa ta kara da cewa, duka wadannan dalilai sun bunkasa ci gaban Afirka, sun kuma taimakawa bunkasar ita kan ta Sin.

Daga nan sai ta yi hasashen cewa, muddin aka ci gaba da inganta hadin kai tsakanin sassan biyu, za a iya kaiwa ga cimma muradun ci gaba mai dorewa na kasa da kasa nan da shekarar 2030.

Jami'ar ta kuma bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka, a matsayin mataki da zai kau da kalubalen da ci gaban Afirka ke fuskanta. A cewar ta kalubalen da nahiyar ke fama da su ta fuskar ci gaba, sun hada da na karancin ababen more rayuwa, da yawan dogaro kan wasu hajoji tsiraru, da karancin jari a harkokin noma, da rauni a fannin zuba jari domin bunkasa kere kere. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China