in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD zai tattauna batun shirin zabe a jamhuriyar Kongo Kinshasha
2018-08-26 15:44:33 cri
Ana sa ran a ranar Litinin kwamitin sulhun MDD zai tattauna game da halin da ake ciki a jamhuriyar demokuradiyyar Kongo (DRC), musamman game da batun shirye-shiryen zabe, wanda shi ne babban dalilin da ya jefa kasar cikin rikicin siyasar da take fama da shi.

Kwamitin zai tattauna ne ta kafar bidiyo da shugaban shirin MDD na samar da zaman lafiya a DRC, Leila Zerrougui, da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na DRC, Corneille Nangaa Yobeluo, da wakilan diplomasiyya.

Ganawar kwamitin MDDr ya biyo bayan sanarwar da shugaban kasar Kongo Kinshasha Joseph Kabila ya bayar ne inda ya ayyana cewa ba zai sake tsayawa neman wa'adin mulki na uku ba.

Kabila, wanda ya daure mulkin kasar a shekarar 2001 bayan an yiwa mahaifinsa Laurent Kabila kisan gilla, a bisa dokokin tsarin mulkin kasar bai halasta ya sake neman tsayawa takara ba bayan karewar wa'adin mulkinsa tun a watan Disambar shekarar 2016.

Ya kamata a gudanar da zaben kasar ne a watan Nuwambar 2016 domin zabar wanda zai gaji mista Kabila, amma saboda samun jinkiri da saba alkawura na rashin gudanar da zaben da aka tsara gudanarwa a karshen shekarar 2017. Daga karshe dai an amince za'a gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Disambar wannan shekara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China