in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana takaici game da matakin Amurka na daina tallafawa hukumar UNRWA
2018-09-01 17:06:08 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana takaici game da matakin Amurka na daina tallafawa hukumar majalisar dake bada tallafin jin kai ga 'yan gudun hijirar Falasdinu.

Antonio Guterres ya bayyana UNRWA a matsayin muhimmiyar hukumar dake tallafawa 'yan gudun hirar Falasdinu tare da bada gudummuwa ga tabbatar da zaman lafiya a yankin, da samar da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya da kuma biyan sauran muhimman bukatun 'yan gudun hijirar.

A don haka, ya yi kira ga sauran kasashe su taimaka su cike gibin kudi da hukumar ke fuskanta, domin ta ci gaba da gudanar da ayyuakanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China