in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin mota ya hallaka mutane 11 a Najeriya
2018-08-23 09:52:30 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 11 ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 16 kuma suka jikkata, sanadiyar wani hadarin mota da ya faru a daren ranar Talata a kusa da garin Kontagoran jihar Neja dake yankin tsakiyar Najeriya.

Wani kwamandan hukumar kare aukuwar hadurra a titunan Najeriya Abdullahi Ibrahim ya bayyana cewa, mutanen sun gamu da ajalinsu ne nan take lokacin da motar bas din da suke ciki mai daukar fasinjoji 27 ta yi taho mu gama da wata motar dake zuwa. An kuma garzaya da mutane 16 da suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa don a yi musu magani.

Jami'in ya ce hadarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce kima da wuce motoci ba bisa ka'ida ba da direbobin ke yi a kan hanya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China